Hukumar kidayar jama’a ta kasa (NPC) ta ce wasu ‘yan Najeriya ba sa son a kidaya su a kidayar shekarar 2023.
A ranar Juma’a a Ebonyi, NPC ta bayyana hakan a cikin kalubalen da hukumar ke fuskanta.
Kwamishinan tarayya, Darlington Okereke ya yi bayani game da aiwatar da gwajin kidayar yawan jama’a da ƙidayar gidaje da akayi a jihar.
Jami’in ya tabbatar da cewa hukumar za ta yi abun da ya dace a lokacin babban kidayar jama’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: An tsaurara jami’an tsaro a kwayar birnin Kano, tare da rufe wasu hanyoyi
Okereke ya ce horar da ma’aikata da bayar da shawarwari na daga cikin dabarun da aka dauka.
Masu ƙididdigewa 90 da masu sa ido tara ne suka shiga cikin ƙidayar gwajin wamda ya kunshi – ƙidayar gidaje da jerin sunayen gidaje – da aka gudanar daga 13 ga Yuli zuwa 15 ga Yulin shekarar nan.
Okereke ya ce kalubalen sun hada da rashin ’yan uwa da za a lissafta, da kin amincewa da wasu mutane, da rashin wurin kwana ga ma’aikatan hukumar.
“Za mu sake tsara dabarun ci gaba da ilmantar da jama’a da kuma kafa kwamitin wayar da kan jama’a na Ebonyi, da dai sauransu,” in ji shi.
A wnai labarin kuma na daban.
Ina Goyon Bayan Yunkurin Tsige Shugaba Buhari— Gwamna Ortom
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yabawa majalisar dokokin kasar nan dangane da baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida na kara kaimi wajen yaki da rashin tsaro ko kuma su iya tsige shi.
A ranar Talata, 27 ga watan Yuli, 2022, jam’iyyar PDP, majalisar dattawa karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Philip Aduda, ta fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewa da gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Daga baya Aduda da takwarorinsa sun yi jawabi ga kungiyar ‘yan jarida ta Majalisar Dattawa inda suka ba da wa’adin makonni shida da su ka fara shirin tsige Shugaba Buhari idan ya kasa kawo karshen rashin tsaro a kasar.
Gwamna Ortom ya yi wannan yabon ne a ranar Juma’a, 29 ga Yuli, 2022 a masaukin Gwamnan Jihar dake Abuja, a lokacin da ya karbi tawagar wasu ‘yan Majalisar Dokoki ta kasa karkashin jagorancin Aduda da suka zo yi masa bayani kan lamarin.
Gwamnan ya bayyana matakin da majalisar dattawa da ta wakilai suka dauka na tsige shugaban kasar a matsayin hali irin na masu kishin kasa, kuma ya yabawa wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da suka zabi yin abin da ya dace.
A cewar Ortom, Buhari ya yi kasa a gwuiwa da yadda ‘yan Najeriya ke zato wajen magance kalubalen tsaro da shawo kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan, don haka akwai bukatar a ba da dama ga mutum wanda ya cancanta.
Tun da farko Aduda ya shaida wa Ortom cewa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar PDP a yankin Arewa ta tsakiya, tawagar ta ga ya dace ta yi masa bayani kan matakin da majalisar dokokin kasar ta dauka na tsige shugaban kasar.
Ya shaida wa Gwamnan cewa duk da cewa Majalisar Dattawa ce ta fara yunkurin tsige shi, amma Majalisar Wakilai da kuma dimbin ‘ya’yan Jam’iyyar APC sun shiga cikin wannan yunkuri.
Ziyarar Aduda ya samu halartar Sanata Orker Jev da Hon Samson Okwu da dai sauransu