Hukumar dake yaki da cututtuka ta kasa watau (NCDC), ta sanar da cewa mutane dari hudu da saba’in da tara ne suka rasa rayukansu sanadiyyar barkewar cutar Kwalera a jahohi sha takwas dake kasar nan.
Hukumar tace, tun dai farkon wannan shekarar, kimanin mutane 19,305 suka kamu da cutar, sannan cutar ta yadu har zuwa jahohi 18 dake wannan kasar.
Kamar yadda Jaridar daily trust ta wallafa a shafinta
Jahohin da suka kamu da wannan cutar Kwalera sun hada da Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, Kano, Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Niger, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara da birnin tarayya Abuja (FCT).
Tun daga watan July 11, 2021, mutane 19,305 duk da wadanda suka rasa rayukansu 479 hukumar ta kididdige a jahohi sha takwas suka kamu.
KARANTA:- Sakataren gwamnatin tarayya Tijjani Umar ya gargadi sabbin ma’aikatan 42 da su rike sirri.
Kamar yadda rahoton yazo, kaso 11 cikin Mutanen da suka kamu yan kimanin shekaru 5-14, inda kaso 52 maza ne sannan kaso 48 mata ne.
Hukumar tace daga karshen watannan jahohin Bauchi, Kano Jigawa da Kwara. Sune suke da kaso mafi yawa da suka kamu da cutar.
Kamar yadda hukumar ta wallafa, tace mutane 31 ne suka mutu a tsakanin 5-11 July, 2021.
Cutar Kwalera dai, cuta ce wadda take haifar da gudawa wadda kwayar bacteria mai suna vibrio coleri ke haifarwa.
Alamun cutar sun hada da yawan amai, rasa ruwan jiki, haifar da matsalar koda, yawan fitar da farin ruwa, yawan jin kasala.
A wani labarin
Yan bindiga sun shiga Kauyen Zurmi sun raunata Mutane uku sun kwashe shanu da dama
Yan bindiga sun afka cikin garin Zurmi wata Karamar hukumar ce dake Zamfara, inda suka jikkata mutane uku, sannan suka tafi da garken shanu wanda ba’a san adadinsu ba.
Sun kuma shiga Kauyen Jaye dake karkashin Karamar hukumar Zurmi dake Jahar Zamfara.
Yan bindiga dai sun afkawa garin ne da nufin hallaka mutane sannan da lalata kayayyaki su, tare da tafiya da duk wanda suka samu, sai dai Yan Sakai sun fatattake su.
Wani shaidar gani da ido ya bayyanawa gidan talabijin na Tvcnews cewa, a yanzu haka ana cigaba da kula da wadanda suka samu raunika a wani asibitin da ba’a bayyana sunansa ba.
A wancan satin dai kauyukan dake Karamar hukumar ta Zurmi, sun sha addaba wajan Yan ta’addan.
Jaridar Tvcnews, tayi kokarin samu wani rahoton daga bakin kwamishinan Ƴansandan na Jahar amman abun yaci tura, bai dauki kiran ba.