Shugaban Hukumar Sadarwa ta ƙasa Farfesa Umar Ɗanbatta ya bayyana cewar sama da layukan sadarwa na mutane miliyan 180 suka haɗa shi da lambar su ta shaidar ɗan ƙasa wato-NIN.
Ɗanbatta ya bayyana haka a ranar Talata a lokacin wani taro a Abuja, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutanen Kaduna za su yi kukan rashin El Rufa’i idan ya bar Mulki ~Cewar Sanata Uba Sani
Dayake jawabi ga masu ruwa da tsaki, Shugaban Hukumar yace haɗa SIM da NIN ya sanya an samu nasarar gudanar da hakan, biyo bayan ƴan Nigeria miliyan 64 da Hukumar ta basu shaidar katin ɗan kasa a kundin ajiye bayanan ta.
Shugaban Hukumar a kwanakin baya, yace samun mutane 1,500 da ake yiwa rajista daga masu amfani da wayoyi, yawan mutanen na ƙaruwa.