Kimanin yara dubu 90,000 ne basa zuwa makaranta a Jahar Anambra, a cewar wani bincike da wata hukuma tayi mai suna ECID.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da cibiyar kula da cigaban ilmi ta Jami’ar Nigeria Nsukka, wanda shugaban ta ya yi Dr Ben Nwosu a Awka a wani taron horaswa wanda Hukumar ECID ta gudanar.
A cewar Professor Nwosu, ya bayyana cewar ƙididdigar da ta nuna haka abun damuwa ne ga Jahar Anambra, ganin cewa jahar na ɗaya daga cikin jahohi, da suka amfana ta fuskar ilmi a ƙasar, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ogun: INEC Ta Koka Da Karancin Masu Yin Rijistar Zabe Ta Kafar Sadarwa
Yace bincike ya nuna cewa, iyaye suna biyan ƙuɗaɗen makaranta ga ƴaƴansu, duk da kawo dokar ilmi kyauta da gwamnatin jihar ta kawo.
Ya kara dacewa “abun damuwa ne musamman ta fuskar ƙididdiga, Anambra na ɗaya daga cikin inda ta amfana ta fuskar ilmi. Abun yafi damuwa idan kaje kaga tazara tsakanin ilmin ƙauye da manyan birane.”
Dr Nwosu ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jahar data gudanar da ƙididdiga a makarantu, domin gano yanayin gine-gine, da ma’aikata, da bayanai a ɓangaren ilmi, domin kawo gyara da tsare-tsare gami da kasafin kuɗi a Jahar.
Dayake maida jawabi akan bayanan da aka gabatar wanda suka nuna akwai yara marassa zuwa makaranta, Kwamishinan Hukumar Yaƙi da cin hanci da rashawa Mark Okoye, yace binciken zai taimaka wa Gwamnatin Jahar wajen tsare-tsare, inda ya jaddada cewa, zai haɗa hannu da shuwagabannin Ma’aikatu wajen magance wasu matsala