Wata budurwa ta wallafa bidiyonta yayin da take yaba wa saurayinta kan yadda ya sauya mata rayuwa ta koma ‘yar gayu sosai, majiyarmu ta Legit.ng ta bayyana hakan.
A wani bidiyo wanda aka wallafa a shafin thatblackwoy ranar Talata, 10 ga watan Janairu, an ga yadda yake nuna farincikinta a kan lamarin.
KU KARANTA: Budurwa ‘yar Afirka ta yi wuff da zuciyar Bature, ya biyota ƙauyensu
A bidiyon, budurwa ta wallafa hotonta kan yadda take a baya kafin ta hadu da saurayinta da kuma yadda yanzu ta sauya.
Bidiyon ya nuna yadda saurayinta ya yi matukar hidimta mata da kudinsa wanda a baya ko kyau ba ta da shi.
An ga wasu jemammun sutturu a jikinta a hotonta na baya, wanda yanzu kuma aka ga yadda fatarta take sheki tare da walkiya.
Ta sauya gabadaya tamkar ba ita bace a baya, kuma ta bayyana dalilin sauyawar ta ta. Nan da nan mutane suka yi caa kowa yana tofa albarkacin bakinsa kan irin wannan kokarin da saurayin ya yi.
Yayin da wasu ke yaba mata kan yadda ta bayyana gaskiyar bayani dangane da rayuwarta, wasu kuma sun yaba wa saurayin.
Wasu kuma sun yi fatan Ubangiji ya kawo musu irin shi don ya sauya tasu rayuwar.
Bidiyon Tulin Kayan Auren Da Aka Kawowa Wata Kyakkyawar Budurwa Ya Ɗauki Hankula
Wata budurwa ƴar Najeriya ta ɗauki hankulan mutane da dama bayan ta nuna kayayyakin da mijin da zata aure ya kawo a matsayin kayan sadaki.
Budurwar ƴar Najeriya ta bayyana irin sha tara ta arziƙi da wanda zata aura ɗin ya kawo domin biya a matsayin kuɗin sadaki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
A cikin bidiyon wanda wani mai amfani da @amyspecialabacha2 ya sanya a manhajar TikTok, an nuna budurwar cikin ƙasaita ta ɗauki hoto a cikin tulin kayan sannan ta yabawa mijin da zata aura kan yadda ya zo cikin shiri domin biyan kuɗin auren ta.