Gwamnatin jihar Kano a karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta karbi allurar rigakafin Korona 209, 520. Rahotanni sun nuna cewa a lokacin da yake karbar allurar rigakafin a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, a madadin Gwamna Ganduje, kwamishinan lafiya, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce allurar rigakafin kashin farko zai fi mayar da hankali ne kan ma’aikatan lafiya da ke jihar.
Jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar lafiya a Kano, Hadiza Namadi ta tabbatar da batun karbar riga-kafin.
Sannan nan ba da jimawa ba za a yi wa gwamanan jihar Abdullahi Umar Ganduje allurar rigakafin.
Sai dai kwamishinan ya ce kwamitin yaki da cutar ta korona a jihar nan gaba zai sanar da lokacin da za a fara riga-kafin ga kowa da kowa a jihar.