Shugaban Kasa Buhari ya nuna takaicinsa dangane da mummunar asarar rayukan da aka yi a Katsina da Borno cikin makon nan, inda ‘yan bindiga da Boko Haram suka kashe kusan mutum 200 cikin kwanaki uku.
A jawabin da ya karanta a Ranar zagayowar dimokuradiyya da kuma cikar mulkin dimokradiyya shekaru 21 a jere ba tare da katsalandan din sojoji ba, Buhari ya nuna alhini, jimami da ta’aziyyarsa ga wadanda abin ya shafa da kuma kasa baki daya.
A jawabin na sa, Buhari ya nuna cewa dukkan hare-haren biyu, an yi amfani da halin zaman gidan da jama’a ke ciki ne aka kai wa jama’a harin. Ya ce ya bada umurni ga jami’an tsaro a gaggauta kamo wadanda suka yi wannan aika-aika domin a hukunta su.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihohi da kananan hukumomi su kara karfafa tsarin leken asirin fallasa batagari da mugaye a cikin jama’a a duk inda aka gan su ko aka ji duriyar su.