By Abbas Yakubu Yaura
Wasu mazauna jihar Imo da suka yi shirin fita daga jihar Imo domin yin bikin Kirsimeti a ranar Litinin din data gabata, sun kasa gudanar da wannan tafiya saboda fargabar abubuwan ban mamaki da suka saba faruwa na dokar zaman dirshan na masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, a yankin Kudu maso Gabas. .
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa daga harabar wasu manyan kamfanonin sufuri da ke kan titin Egbu da Onitsha dake Owerri.Har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto, wasu daga cikin kamfanonin sufurin basu fito domin gudanar da kasuwanci ba saboda gogewar da suka samu inda jami’an tilasta bin umarnin zama a gida suka kai musu hari tare da kone su.
An ga cewa wasu matafiya sun makale yayin da ofisoshin wasu kamfanonin bas din ba a bude su ba.
An tattaro cewa galibin wuraren da matafiya suka ce suna son tafiya sun hada da; Anambra, Enugu, Benue, Delta, Ebonyi, Umuahia da dai sauransu, musamman jihohin dake makwabtaka da jihar Imo.
Kazalika, Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ma bai bambanta da wasu ’yan Imola da suke sa ran dawowar ‘yan uwansu a ranar 27 ga watan Disamba domin bukukuwan Sallah ba.
Daya daga cikin mazauna yankin da yake son tafiya jihar Ebonyi ya bayyana sunansa da Micheal, ya ce: “Na fito da safe domin in shiga motar zuwa jihar Ebonyi amma akwai motar. Sai suka ce mu jira da misalin karfe 3 na yamma za su yi shirin tafiya.”
Wani wanda ya ce sunansa Chiwendu Okafor, ya ce: “Na fita da sassafe babu abin hawa amma da tsakar rana muka fara ganin abin hawa wasu daga cikinsu har yanzu suna tsoron motsi saboda dokar zama a gida. Inda Suka ce Onitsha ya yi zafi.”
Lamarin bai bambanta da mutanen da suke tsammanin ’yan uwansu za su dawo gida don bikin Kirsimeti ba.