Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 25 ga watan Disamba da kuma Litinin 28 ga wata da kuma 1 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar hutu sakamakon bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin a wata sanarwa da Sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore ya fitar a ranar Laraba.
Gwamnatin ta nemi al’ummar Kirista su yi amfani da wannan lokacin wajen koyon sadaukarwa, hakuri, zaman lafiya da aikata daidai na Yesu Almasihu, wanda gwamnatin ta ce suna daga cikin abin da za su koya a lokacin da suke tunawa da haihuwar Yesu.
Ya kuma shawarce su da su tabbata sun bi ka’idodin dakile kamuwa daga cutar korona a yayin addu’o’i a coci-coci.