Shugaban hafsan hafsoshin tsaron kasar nan Lucky Irabor a ranar Talata ya ce an kama wadanda suka kai harin Owo.
Irabor ya bayyana haka ne a wata ganawa da editoci da shugabannin kafafen yada labarai a Abuja.
A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan an kammala bincike kan lamarin.
Irabor ya ce, “Mun kama wadanda suke da hannu a wannan aika aika a Owo.
“Niyyata ce in gabatar da su ga jama’a, amma saboda binciken da ake yi, sai na canza shawara.”
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa a ranar 5 ga watan Yuni, ‘yan ta’adda sun kai hari cocin St. Francis Catholic Church, dake titin Owaluwa, agarin Owo, a lokacin da suke gudanar da ibada a cocin.
A wani laabrin kuma na daban.
Zaben Kenya: Fiye da Mutum miliyan 6 ne suka kada kuri’a kawo yanzu—- Hukumomi
A cikin wani sabon rahoto da hukumar zaben zaben kasar, Kenya ta fitar ta bayyana cewa zuwa tsakar rana, mutane miliyan shida da digo biyar 6.5 ne za su kada kuri’a a zaben kasar.
A cewar alkalan zaben kasar, wannan adadi da aka ambata ya kai sama da kashi 30% na wadanda suka yi rajistan zabe. Za a ci gaba da bude rumfunan zabe har zuwa karfe biyar na yammacin agogon kasar.
Rahotanni daga sassa daban-daban na kasar sun nuna cewa kawo yanzu ba a samu fitowar jama’a ba, idan aka kwatanta da zabukan da suka gabata a baya.
Hukumar ta yi ƙoƙarin magance matsalolin dake tattare da na’urar dake tantance yatsu kowani dan’adam, da aka ruwaito ana aiki da shi a wurare daban-daban da ake gudanar da zaben.