Rahotanni da suke shigowa Jaridar Dimokuradiyya daga kasar Afrika ta Kudu sun nuna cewa; jami’an ‘yan sandan Afrika ta Kudu sun tabbatar da kama mutum 80 da ake zargin suna da hannu wajen kashe ‘yan Nijeriya a kasar, sannan sun tabbatar da kashe karin mutum biyar a wani rikici da ya barke a biranen Johannesburg da babban birnin kasar na Pretoria a ranar Talata.
Wadanda ake zargi da tada rikicin, sun rika farfasa shagunan baki a kasar. Sannan titin Alexander masu tada rikicin sun kona shagunan mutane da farfasa gilasan da ke jikin shagunan.