Rahotanni dake shigowa Jaridar Dimokuradiyya daga birnin tarayya Abuja, sun nuna cewa masu zanga-zangar tir da Allah wadai da kashe ‘yan Nijeriya a Afrika ta Kudu sun fara kone-konen tayoyi da allunan talla a titin zuwa filin jirgin saman Abuja, inda wannan ya haifar da cunkoson ababen hawa a yankin.
Masu zanga-zangar a Abja sun nufi shagon Shoprite dake titin zuwa filin jirgin saman Abuja, sai dai shaidun gani da ido sun ce; jami’an ‘yan sanda sun hana su isa ginin. Inda su kuma masu zanga-zangar suka fara kone-konen tayoyi da allunan talla.
Wannan lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin zuwa filin jirgin saman, inda ya haifar da mutane suna ta juyawa.
Tun bayan da labarin kashe ‘yan Nijeriya ya ba zu a tsakanin ‘yan Nijeriya, ‘yan Nijeriya suka fara yiwa kamfanonin Afrika ta Kudu musamman shagunan Shoprite da MTN barazana.