By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Yobe, Honarabul Mai Mala Buni, ya amince da daukar ma’aikatan harhada magunguna guda 27 aiki domin bunkasa ma’aikata a fannin kiwon lafiya a jihar.
Gwamna Buni ya amince da hakan ne biyo bayan bukatar da Hukumar Kula da Magunguna da likitocin Jihar ta yi.
A cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan, Mamman Mohammed ya fitar jiya Alhamis, yace daukar ma’aikatan harhada magunguna na da nufin samun kwararrun ma’aikatan da ake bukata domin aiyuka masu inganci da kuma karin inganta harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Bisa amincewar, gwamnati zata dauki dalibai 23 da suka kammala karatun harhada magani da kuma kwararrun likitocin harhada magunguna hudu, domin inganta aikin da hukumar ke bukata.
Gwamnan ya kuma amince da sanya dalibai 23 da suka kammala karatun harhada magani a kan sikelin albashi na CONHESS 9/2 yayin da masu fasaha za a sanya su a sikelin CONHESS 7/2.
Daukar ma’aikata dai ta yi daidai da yunkurin gwamnatin Gwamna Buni na samar da harkar isar da lafiya ga ‘yan kasa.