By Abbas Yakubu Yaura
kimanin Sama da kwararrun likitoci 3000 ne suke ci gaba da yajin aiki a Angola wadanda suke neman karin albashin yanayin aikin su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kungiyar likitoci ta kasa ta sanar da tsawaita yajin aikin data fara a makon jiya.inda Kungiyar ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki 30 duk da cewa ta fara tattaunawa da gwamnatin.
A cewar kungiyar likitocin, majinyata marasa lafiya ne kawai zasu ci gaba da karbar magani a asibitocin gaggawa inda kashi 50% na ma’aikatan dindindin ke halarta.
Sannan tace Dangane da lambobi na hukuma akwai kwararrun likitocin 5.200 dake aiki a kasar.
Kazalika Barkewar cutar Covid 19 ta kara matsin lamba kan tsarin likitan daya rigaya ya yi rauni a Angola ta sami rahoton kamuwa da cutar 65 400 da kuma mutuwar kusan mutane 1700.
Comments 1