Wata Matashiya da ta yi amfani da man sauya launin jiki da aka fi sani da bleaching a turance, ta ce fatarta ta sauya ta inda har mahaifinta ma ya kasa gane ta.
Matashiyar ta ce ta fara amfani da man ne na kusa tsawon shekara goma.
Matashiyar mai suna Grazia daga jihar Bradford na yammacin Yorkshire ta ce ta fara amfani da man ne tun tana shekara 18 kuma babu kakkautawa.
Sai dai binciken da tashar BBC ta yi ya tabbatar da cewa ana saida man ne a bayan fage a ɗaiɗaikun shaguna.