An yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta soke ƙarin da aka yi na farashin man fetur da wutar lantarki ko ya fuskanci tirjiya daga talakawan ƙasar nan.
Wata ƙungiya rajin kare muradun Arewa (CNG) ta buƙace shi ya mayar da farashin mai N145 na wutar lantarki kuma N23 domin kaucewa gangamin ƙalubalantar ƙarin farashin a faɗin Najeriya.
Kakakin ƙungiyar, Abdulaziz Suleiman ya ce, “Matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka a ’yan kwanakin nan na ƙara farashin muhimman abubuwa kamar wutar lantarki da man fetur ya fuskanci Allah-wadai daga al’ummar kowanne ɓangare na Najeriya.
“Bayan damuwa da nuna takaici kan irin wannan matsin da aka jefa ’yan ƙasa, CNG ta yi taro a Kaduna domin duba halin tsadar rayuwa, halin talauci da kuma matsalar rashin tsaro.
“Taron ya tattauna kan yadda hukumomi suka kasa haɓaka tattalin arziƙi, tsaro da kuma haɗin kan ƙasa, waɗanda su ne suka zama ummul-aba’isun halin da jama’a su ka tsinci kansu.
https://dimokuradiyya.com.ng/matsin-rayuwa-ya-janyo-an-gudanar-da-zanga-zanga-a-jihar-osun/
“Abin takaici ne matuƙa cewa duk da irin alƙawuran da gwamnati mai ci take yi na yaƙi da cin hanci da rashawa, kusan za a iya cewa gwamma jiya da yau musamman in aka yi la’akari da matsayin Najeriya a ma’aunin yaƙi da rashawa na duniya”, inji sanarwar.
Har wa yau, ƙungiyar ta Arewa ta ce an yi wa gwamnati mai ci duk irin uzurin da ya kamata, duk da cewa har yanzu ita ba ta yi abin da ya kamata ba.
Ƙungiyar ta lissafa abubuwa da dama da farashinsu suka yi tashin gwauron Zabi kamar harajin kayayyaki na VAT daga kaso biyar cikin 100 zuwa 7.5, farashin shinkafa, masara, takin zamani, kuɗaɗen ƙasashen waje da sauransu.
A cewar Kungiyar ƙare-aren sun kara taimakawa wajen kara jefa alu’mma cikin halin matsi da takura.
Ta ce abin takaici ne yadda gwamnati ta damka ragamar kayyade farashin mai kacokam a hannun kungiyar dillalai ta IPMAN, wanda hakan ke nuna gazawarta.