Ko Kaɗan Matsalar Tsaron yankin Kudu Maso Gabas ba akan Makiyaya take ba – Miyetti Allah
Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya a ranar Talata tace matsalar tsaro dake akwai a Ƙasar musamman a yankin Kudu Maso Gabas ba mambobin ta ake so aga ƙarshen su ba.
Shugaban Ƙungiyar na Shiyyar Kudu maso Gabas Alhaji Gidado Siddiki ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a Enugu mai taken “Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah tana maida jawabi ne akan wani rahoto a Kafafen Yaɗa Labaru cewa an samu hatsaniya tsakanin ta da ƴan Ƙungiyar IPOB akan ƙine motar Shanu a Jahar Anambra”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan fara aiki ne daga awata ta farko a Ofis — Cewar Wani Ɗan Takara
Yace matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas bawai wani matsala bace ta daban kamar yadda lamarin yake a wasu sassan Ƙasar nan.
“Akwai hujjoji cewa yadda Makiyaya suka sha wahala akan ayyukan tsageru da sauran ƴan Najeriya, wanda kayayyakin Gwamnati dana ƴan Kasuwa sun ɓata a hannun waɗannan mutane.
Siddiki yace Ƙungiyar MACBAN bata haɗi da abinda ake bayyanawa na hatsaniya tsakanin su da wata ƙungiya.
“A yayinda Ƙungiyar MACBAN ke cigaba da neman a zauna lafiya a tsakanin ƴan Najeriya da ƙabilu, muna kira ga Gwamnati data zaƙulo masu tada zaune tsaye a tsakanin ƙabilu masu karya doka a faɗin Ƙasar”, Inji shi.
Comments 1