Duk da bullar Coronavirus a kasashen Afrika 52, amma har yanzu akwai kasa biyu da babu cutar, wanda ya hada da kasar Lesotho da Comoros.
Rahotanni sun bayyana cewa; Akalla mutum 16,000 ne ke dauke da cutar Korona a kasashen Afrika 52 da cutar ta bullla. A yayin da gwamnatocin Afrika daban-daban ke daukar matakai wajen ganin an dakile yaduwar cutar.
A bayanan baya-bayan nan da Jami’ar John Hopkin da sashen dakile cuta ta Afrika kan cutar COVID-19, sun tabbatar da cewa alkaluman na karuwa ne a kowacce rana duba da yadda kasashen ke ci gaba da gano masu dauke da cutar.
A Afrika mutum 16,265 aka tabbatar suna da cutar, a yayin da mutum 873 suka rasa ransu, sai kuma mutum 3,235 suka warke daga cutar yayin da kasashen Afrika 52 cutar ta bulla. Inda kuma kasashe biyu a Afrika cutar ba ta bulla ba, wanda ya hada da; Lesotho da Comoros.