KUN SAN YAUSHE ZAA FARA HASKA SHIRIN LABARINA?
DIMOKURADIYYA:Shirin LABARINA, ya sami karbuwa nan gida Najeriya har ma kasashen ƙetare wane tabbaci kuke da shi cewar wanda kuke dauka zai farantawa masu kallo kamar wanda ya gabata?
SAIRA: Eh daukakar shiri wannan daga Allah ne, amma mun yi Iya kokarin mu don ganin mun fita kunyar mutane shi yasa muka kwashe tsawon kusan watanni 3 muna ta aiki, sai dai rubutun Labarin shine yafi daukar dogon lokaci amma yanzu nesa ta zo kusa.
DIMOKURADIYYA:Masu bibiyar shirin sun ƙosa, ko yaushe zaku fara haska shirin?
SAIRA:Eh Shuaibu, kaga yanzu wata mai Albarka na Ramadan zamu shiga, duk da kusan mun kammala amma yanzu zamu tattara mu koma Ibada gaskiya bazamu iya fara haska shi a cikin watan Ramadan ba.
DIMOKURADIYYA:To yanzu zamu iya yi ma mutane Albishir cewar zaa fara haska shirin a matsayin Goron Sallah kenan?
SAIRA:Kwarai da gaske muna saka ran zamu fara haska shi da Sallah a matsayin Goron Sallah.
DIMOKURADIYYA: Shirin farko an yi waƙa wacce ta sami karbuwa, shin wannan sabon da kuke dauka ma akwai waƙa a ciki?
SAIRA: Waƙoƙi kai, sosai ma tabbas akwai waƙokin da zaa yi a sabon da muke dauka.
DIMOKURADIYYA: Kuma sun yi daɗi kamar wadancan na farko?
SAIRA:Eh maganar waƙa mai daɗi ko akasin haka wannan daga Allah ne amma mun yi kokari.
DIMOKURADIYYA:Shirin na farko kusan mafi yawa baƙin fuskoki kuka yi amfani da su har shirin ya sami karbuwa sai dai da alama yanzu kun saka tsofaffin Jaruman Kannywood ya aka yi haka?
SAIRA:Eh wannan ba wani matsala bane yanayin salon Labarin ne yazo haka, ai ko yanzu sabbin fuskoki masu kallo zasu gani a cikin shirin.
DIMOKURADIYYA:To wanzu a wace kafa zaku haska cigaban shirin na LABARINA, tunda rahotanni sun gabata da alama ma kun yi hannun riga da tashar Arewa24??
SAIRA:A’a babu wata matsala da muka samu da tashar Arewa24, mun dai kulla yarjejeniyar aiki da su kan zasu haska zango na 1 dana 2 kuma yarjejeniyar ta ƙare, saboda haka sai mun sake zama da su idan mun daidaita zamu kulla yarjejeniyar haska zango na 3 dana 4?
DIMOKURADIYYA: Idan baku daidaita ba fa a wace kafar zaku haska?
SAIRA:Shuaibu, ka cika tambaya da yawa, eh bazan iya cewa komai ba a kan wannan sai mu jira lokaci.
DIMOKURADIYYA:Masu hasashe na cewa Lukman, ne zai dauke Sumayya?
SAIRA:Hahahahahha Shuaibu, mu ƙara hakuri shirin zai fayyace komai.
DIMOKURADIYYA: Aminu, a wadanne Jihohi kuke daukar Shirin?
SAIRA:Sanin inda aka dauki shirin bashi bane mafi muhimmanci, zaka iya zuwa ka ƙafa Kano a ko wace Jihar abun da ake so shine gamsar da masu kallo.
DIMOKURADIYYA