Tun bayan da guguwar marka-markar ƙwallayen da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta yiwa Barcelona a wasan kusa daba kusa dana ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai yasa Barcelona ta sallami mai horas warta inda ta kawo sabon mai horas wa wato tshohon ɗan wasanta Roland Koeman ɗan asalin ƙasar Netherland.
Daga zuwansa ya bayyana sabon tsarin da yazo dashi na sauya akalar wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da kuma Cesar zai tarkata wasu tsofaffin ‘yan wasan ya kora daga Barcelona musamman waɗanda shekarunsu ya haura talatin ciki harda Luis Suarez, tuni kuma Rakitic ya koma Sevilla inda shikuma Aturo Vidal ya kammala komawa Inter Milan dake ƙasar Italiya.
Shikuwa Suarez ya shirya komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus amma kuma da yaje can ƙasar ta Italiya sai ya gamu da cikas inda bashi da fasko na ƙasar Italiya, haƙafayasa suka bayyana cewar sun fasa sayensa inda babu arziki ya tattaro komatsansa ya dawo birnin Camp Nou dake ƙasar ta Andalus. Saidai duk a haka ba a barshi ya ci gaba da zama a Barcelona ba.
Bayan hakan ta faru aka cimma matsaya tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da Athletico Madrid inda Suarez ya amince ya koma can inda sukuma suka tura ɗan wasansu matsayin aro zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus inda daman tsohuwar ƙungiyar sa ce, a yanzu dai za a iya cewa ta tabbata Luis Suarez zaici gaba da zama a ƙasar Andalus domin ci gaba da buga gasar Laliga da Copa del Rey da kuma kofin gasar zakarun nahiyar turai amma ba’a Barcelona ba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid dake birnin Madrid.
Saidai abin tambayar anan shine ana ganin cewar Barcelona tana ta sayar da manya-manyan ‘yan wasanta amma kuma har yanzu batayi siyayyar azo a gani ba, tunda ana ganin cewar duk tsakiyar Barcelona babu kamar Rakitic amma kuma sun sallame shi, sannan duk ‘yan wasan gaban Barcelona babu kamar Suarez amma shima sun sallame shi kuma basu kawo wani ba.
Haka zalika ana ganin Barcelona tana tuya tana mantawa da albasa ganin cewar har yanzu akwai ‘yan wasan da suka gaji kuma shekarunsu ya ja sosai kuma bata da niyyar sayar dasu kamar Gerrard Pique da Sergio inda ake ganin cewar su masu uwa a kusa da murhu ne shiyasa ba a sallame su ba, amma masana na ganin cewar Gerrard Pique ya saba ɓallowa Barcelona ruwa tun a shekarun baya musamman wasu ƙwallaye da aka dinga zabgawa Barcelona da dama ana ganin cewar laifinsane.
Shin ko wannan sabon mai horas war zai kai Barcelona ga tudun mun tsira ganin cewar a tarihinsa duk ƙungiyar ƙwallon ƙafan da yaje korarsa akeyi inda ba a wanye wa dashi lafiya, gashi kuma a yanzu Barcelona tana cikin matsananci rashin tabbas inda gigitawar da Bayern Munich tayimusu bai sakesu ba kwata-kwata.
Tuni aka fara fafata wasannin gasar Laliga amma ita ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona bata buga wasa ba inda an shiga mako na biyu da fara gasar, sai dai ana ganin cewar kamar wasan zaizomata da dama-dama tunda abokiyar hamayyarta wato Real Madrid kunnen doki ta buga a wasan farko inda ta tashu babu ci tsakaninta da Real Sociedad.
Suarez yazo Barcelona daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool a shekarar 2014 inda ya buga wasanni guda 191 sannan ya jefa ƙaallaye guda 147, haka Suarez bai tsaya nan ba ya lashe kofuna guda 13 tare da Barcelona ciki harda gasar zakarun nahiyar turai da kuma gasar Laliga guda 4 da gasar Copa del Rey guda 4 da gasar Super Cup guda 1 da gasar Supercoper de Espana guda 2 da gasar zakarun nahiyoyi guda 1.