Shahararren ɗan wasannan wanda ya addabi duniya musamman a abin da ya shafi harkar wasan ƙwallon ƙafa wato Leonel Messi zai fuskanci wani ƙalubale a wasan da ƙasarsa ta haihuwa wato Argentina zata fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ƙasar Bolivia.
Messi dai tunda yake kusan za a iya cewa yakan jefa ƙwallo aka kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa idan yana buga wasa musamman a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, haka zalika Messi yakan jefa ƙwallo kusan a kan kowacce ƙasa idan yana fafata wasa a ƙasarsa ta haihuwa wato Argentina.
Amma kuma har yanzu akwai ƙasashen da Leonel Messi ya kasa zurawa ƙwallo haka zalika har yanzu akwai ƙungiyiyin ƙwallon ƙafan daya kasa zurawa ƙwallo a raga duk da irin ragargazar da yake yiwa kowacce ƙungiya kokuma kowacce ƙasa idan ya fuskanceta.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafan da Argentina zata fafata wasa dasu a yau wato ƙasar Bolivia gana daga cikin ƙasashen da Leonel Messi ya kasa zurawa ƙwallo a raga duba da cewar Messi ya buga wasa dasu har sau biyu a shekarun baya inda kwata-kwata Argentina ta kasa samun nasara akan Bolivia. Tunda Messi ya fara bugawa Argentina wasa ya fuskanci ƙasar Bolivia sau biyu, inda suka yi haɗuwar farko a shekarar 2009 inda Bolivia ta ragargaza Argentina daci 6 – 1. Sannan kuma a shekarar 2013 sun sake fafatawa a tsakaninsu inda aka tashi kunnen doki wato 1 – 1.
Abin tambaya a nan shine ko Leonel Messi zai iya karya wancan lago na ƙasar ta Bolivia a wasan da zasu kara da Argentina?. Amma kuma idan za abi salsala mafi yawan ƙungiyoyin ƙasashen Latin sukan baiwa Argentina wahala idan ana fafata wasa duba da yadda ake gumurzu idan za a kara da juna.
A nahiyar ta Kudancin Amurka dai ana fafata wasannin neman cancantar buga gasar cin kofin duniya da za ayi a ƙasar Qatar a shekarar 2022, amma a wasan farko da ƙasar ta Argentina ta fafata tasha da kyar a hannun ƙasar Ecuador daci 1 da nema kuma Messi ne ya sami nasarar jefa ƙwallon ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida.