Tun lokacin da shahararriyar jarumar nan ta ƙasar Indiya wato Priyanka Chopra ta tsunduma soyayya da saurayinta wato Nick Jonas mutane suke ta yin surutu cewar kawai wayo zata yimasa ta cuceshi ganin cewa shi yaro ne ɗanye ta girmeshi.
Inda a tsakaninsu akwai tazarar shekaru 10 inda yanzu tana da shekaru 38 a duniya shikuma yana da shekaru 28 wato itace ta girmeshi da shekaru goma kenan, ganin haka ake ta maganganu akan cewar kawai wayo zatayimasa don ta ganshi ɗanyen saurayi dashi.
Ana haka soyayyarsu tayi zafi sosai har suka ƙara shaƙuwa inda soyayyarsu ta kai ga yin aure inda sukayi aurensu a shekarar sannan kuma tun bayan auren mutane suke ta ƙaanan maganganu cewar zata sa ya tsufa da wuri kuma suna ta cewar tabbas aurensu bazai yi ƙarko ba.
To amma Prinyanka ta fara nunawa duniya cewar sufa yanzu soyayyarsu ta fara daɗi inda take wata magana:
“Wato duk daman shiru nayi da irin maganganun da mutane suke cewa a kan soyayyarmu da mijina suna ganin cewar aurnmu bazaije ko inaba, to ku sani cewar kullum ni da mijina ƙara son junanmu mukeyi kuma soyayyarmu ƙara girma ta keyi saboda haka ‘yan baƙin ciki sai dai ku mutu”
Jaruma Priyanka dai ta ƙara da cewar duk da shekaru da aurensu ya kwashe suna tare ko yanzu sun baiwa mara ɗa kunya, kuma ta bayhana cewar wannan miji nata shine masoyinta na har abada suna jin daɗin zama da juna.
Sunyi aure a shekarar 2018 inda da shi da ita dukkaninsu jarumai ne a masana’antar ta Bollywood kuma kowannensu yana bayar da gudun mawa yadda ya kamata kuma soyayyar kullum sake zama sabuwa takeyi.