Darkta-Janar na Ƙungiyar Gwamnoni Salihu Lukman ya bayyana damuwa na yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ke kawo cigaba na inganta zaɓuɓɓuka, amma jam’iyyun siyasa sun zama koma baya.
Lukman ya bayyana haka a cikin wata ƙasida daya sanar a Abuja a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewar, aiwatar da gyara a dokar zaɓe, wadda zata bada dama a riƙa tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo, gami da gudanar da zaɓen fidda ƴan takara mataki ne da aka ɗauka masu kyau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindigan da su kayi Garkuwa da Daliban Jami’ar Lafia sun bukaci Milliyan 20
Ya ƙara dacewa duk da an ɗauki matakan domin inganta harkokin zaɓe a kula da zaɓe a ƙasar, amma kula da jam’iyyun siyasa na cigaba da zama koma baya.
“Wannan tsari na koma baya akwaishi a kowacce jam’iyya, na yadda Shuwagabannin siyasa da suke son yin takara na kujerun gwamnati, suna ɗaukar yaran su ne.
“Wanda ke biyayya zai zama shugaba a gwamnati, shi kuma ɗan siyasar zai biyashi na zama delegates a Jam’iyyar, wanda su zasu tabbatar wa mutum da kujerar sa.