osinbajo-speaking-1

Ko Osinbajo Zai Tsallake Tuggun ‘Cabals’?

Bayanai sun fito a tsakiyar makon nan game da abin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ragewa mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo karfi tare da rusa kwamitin da yake jagoranta. Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyanawa ‘yan jarida cewa wasu masu rike da madafan iko a gwamnatin Buhari su na kulle da mataimakin shugaban kasar a ransu tuntuni.

Wasu daga cikin abubuwan da Mai girma Yemi Osinbajo ya rika yi a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari yake jinya a kasar waje ne ya jawo na kusa da shugaban kasar su ke taka sa.

Daga cikin matakan da ya dauka akwai dora babban Alkali mai shari’a Walter Onnoghen a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya, abin da shugaba Buhari ya gagara yi a kasar.

Haka zalika a Agustan 2018, Osinbajo ya dakatar da shugaban hukumar DSS masu fararen kaya, Lawal Daura daga kan matsayinsa inda ya yi wuf ya nada Mathiew Sayiefa a matsayin Magajinsa.

An dauki wannan matakai ne a lokacin da Buhari ba ya kasar, daga baya dai an sauke Walter Onnoghen daga kan kujerarsa, sannan kuma aka canza Mathiew Sayiefa bayan tsige Lawal Daura.

Majiyar ta ce wadanna matakai biyu da Osinbajo ya dauka ne su ka hada shi fada da wasu manyan na hannun daman shugaban kasar. Wannan abu dai bai yi wa wasu ‘yan cikin gidan APC dadi ba.

Akwai rikicin da aka rika yi da Obono-Obla wanda shugaba Buhari ya ba rikon kwamitin da zai karbo dukiyar gwamnati da ke hannun jama’a wanda wasu ke ganin da hannun Osinbajo a rikicin.

Fadar shugaban kasar ta bakin Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa watau Laolu Akande ta yi watsi da wannan rade-radi. Sannan Buhari yace rusa kwamitin EMT alheri ne ga Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *