Dan shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, Muhoozi Kainerugaba, ya fada a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis cewa “tabbas” zai zama shugaban kasa bayan mahaifinsa.
Muhoozi Kainerugaba mai shekaru 48, wanda a baya-bayan nan ya shiga tsaka mai wuyar diflomasiyya da Kenya, masu lura da al’amura dai sun dade suna kallonsa a matsayin wanda zai gaje shi, duk da cewa a shekarar 2013 Kainerugaba ya ce “Shugabancin Uganda ba sarauta ba ce”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Kano Yayi Sabbin Nadin Mukaman Sarauta
“Hanya daya tilo da zan iya gode wa kyakkyawar mahaifiyata ita ce in zama shugaban kasar Uganda. Kuma tabbas zan yi,” Muhoozi Kainerugaba ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.
Yoweri Museveni, mai shekaru 78, wanda ke mulkin Uganda da hannu bibbiyu tun shekarar 1986, zai iya sake zama dan takara a zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a shekarar 2026 mai zuwa.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar 18 ga watan Oktoba, Yoweri Museveni ya bayyana cewa dansa daya tilo wanda shi ma yana da ‘ya’ya mata uku ba zai sake wallafa wani sako a shafinsa na Twitter ba game da al’amuran da suka shafi kasar bayan wasu jerin sakonnin twitter da aka yi ta cece-kuce a farkon Oktoba na barazanar mamaye kasar Kenya.
Shugaban kasar ya ce har yanzu dansa na iya bayyana ra’ayinsa a dandalin sada zumunta, idan har ya takaita ga yin tsokaci kan wasanni, misali.
Sai dai Muhoozi Kainerugaba bai damu ba, inda ya bayyana a shafinsa na Twitter a washegarin ranar: “Ni babba ne kuma ba wanda zai hana ni komai.
A farkon watan Oktoba, dan shugaban kasar ya ba da shawarar cewa za a dauki shi amma bada sojojinsa ba “makwanni biyu” ba don karbe ikon birnin Nairobi babban birnin Kenya ba. Bayan ‘yan kwanaki ya nemi afuwar sabon shugaban Kenya William Ruto.
A ranar 4 ga watan Oktoba, an maye gurbin dan shugaban kasar Uganda a matsayin shugaban sojojin kasa na kasar.
Tuni a cikin 2022, jerin kalaman da Muhoozi Kainerugaba ya yi a shafin Twitter na goyon bayan ‘yan tawaye a yankin Tigray na Habasha, da ke yaki da hukumomin tarayya, sun harzuka mahukunta a Addis Ababa.
A shekara ta 2013, ‘yan sandan Uganda sun kai samame ofisoshin gidan wasu jaridu biyu da wani gidan rediyo bayan wani shiri na sirri da wani Janar din soji ya yi ikirarin cewa shugaba Museveni na shirin baiwa dan sa damar ya gaje shi kuma yana shirin kashe ‘yan adawa.
A wani labarin kuma, Kasashe Hudu Sun Bi Sahun Amurka, Sun Ce Akwai Yuwuwar Kai Harin Ta’addanci a Najeriya
Gwamnatocin kasashen Jamus da Bulgeriya da Ireland da kuma Denmark sun gargadi ‘yan kasarsu kan tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan saboda karuwar hare-haren ta’addanci.
Shawarwarin tafiye-tafiyen ya zo ne kwanaki kadan bayan Amurka, Birtaniya, Australia da Kanada sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja.