Tsohon na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya ce da rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan, ba zai yi mamaki ba idan aka yi garkuwa da Shugaban kasa.
Galadima na mayar da martani ne kan rashin tsaro da kasar ke fama da shi a wata hira da yayi da sashen Hausa na BBC.
Ya ce, “Wadannan ’yan fashin sun wulakanta gwamnatin Buhari. A farkon gwamnati kowa ya ji tsoronsa (Buhari); ya sa ran zai yi jaruntaka kafin yanzu ya fallasa rashin kokarinsa a fili.
“Buhari bai san komai ba, ba zai iya yin komai ba, shi ya sa za ka ga jami’an gwamnati suna kwasar biliyoyin kudi daga dukiyar al’umma kuma babu wanda zai iya hana su.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Za Mu Rufe Tattalin Arzikin Najeriya Idan Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Magance Yajin Aikin ASUU – NLC
Galadima ya kara da cewa idan ‘yan ta’adda za su iya karya gidan yarin Kuje, shi kansa Buharin ba shi da cikakkiyar kariya
Ya ce, “Idan ba a kula ba, ko ba dade ko ba dade za a iya yin garkuwa da Buharin idan aka yi la’akari da yadda ake watsi da al’amuran tsaro.
“Abin da kawai yake da shi a yanzu shi ne ko dai mu ci gaba da addu’a ko kuma mu rike makamai domin neman kariya amma idan muka dogara da wannan gwamnati to tabbas za a kashe mu.
A wani labarin kuma makamancin wannan.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gabatar da rahoton tsaro 44 gabanin harin da aka kai gidan yarin Kuje a Abuja.
A ranar 5 ga Yulin shekarar 2022, ‘yan ta’adda suka mamaye gidan yarin Kuje tare da kubutar da mutane sama da 800 da ake zargi, ciki har da dukkan ‘yan Boko Haram da ke tsare.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayar da gudunmuwar kudirin dakatar da shirin gwamnatin tarayya na haramta amfani da babura a fadin kasar nan.
Abubakar Makki Yelleman na jam’iyar APC daga jihar Jigawa ne ya gabatar da kudirin a zauren majalisar a ranar Talata.
Ya ce: “Kuna iya tunanin abin da ke faruwa yau a Abuja. Zan fada mukj gaskiya. Na ga rahoton DSS. Inda suka bayar da rahotanni 44 kafin harin Kuje. ina so in tabbatar muku da cewa, sai da na duba dukkannin 44 Kuma duk yana da alaƙa da wannan.
“Babu wata al’ummar da abu zai faru kuma ba za mu sami bayani ba, kuma wannan wani bangare ne na bayanan da suka bayar a matsayin abin da ke faruwa, abin da ke faruwa da abin da ba zai faru.”
Wase ya ce, ya kamata a tallafa wa gwamnati don aiwatar da irin wannan yunkuri a cikin al’ummomi masu rauni inda dokar za ta iya bincikar ‘yan fashi, ta’addanci da sauran laifuka.