Wata ‘yar Najeriya ta garzaya har kotu inda ta maka abokinta bayan ya ki cikasa sharuddan aikin da suka kafa, Legit.ng ta ruwaito.
A cewarta ta siya masa babur mai kimar N180,000 amma har yanzu ta ji shiru.
KU KARANTA: Yadda matashi ya kai wa budurwarsa ziyarar bazata, ya sha mamakin abinda ya gani
Ta bayyana cewa ya dai bata N80,000, tun daga nan ya murje ido yace ba zai kara mata ko sisi ba.
Shi kuma ya bayyana hujjarsa ta yin hakan, inda yace akwai mutunci tsakaninsu kuma abokan juna ne, don haka ba zai bata ko sisi ba.
Ganin hakan ne yasa ta lallaba kotu inda ta bukaci alkali ya amsar mata ragowar kudinta dake hannunsa.
Ta sanar da kotun cewa:
“Ya biya ni na watanni biyu daga nan ya dakata. Ya ce bai fahimci abinda nake cewa ba. Ya ce wai a N80,000 na siya, saboda me zan kara N100,000 a kai?
“N80,000 kacal ya ba ni. Kuma har yanzu yana amfani da babur din wurin yin sana’arsa. Ya ce ba zai iya biyana ba kuma ba ya fahimtar abin da nake fadi.”
A bangarensa ya ce:
“Na je wurinta neman taimako ne, sai ta siya babur a N80,000 sai tace in biya ta N180,000. Ni kuma na amince, har kudin kati na bata N2,000. Ai ya kamata ya tausaya min. Ni fa abokinta ne. Kudin ya yi yawa, ba zan iya biya ba.”
Yadda Sule ɗan achaɓa ya cika bujensa da iska bayan budurwar da su ke lalata ta sheƙa lahira
Ana zargin Sule ya kebe da budurwa mai suna Muniat a ranar Juma’a da dare, amma kuma aka neme shi aka rasa bayan an ga gawarta a karamar hukumar Igbogbo Bayeku da ke Jihar Legas, Nigerian Pulse ta ruwaito.
An tattaro bayanai ka yadda mai kula da masaukin bakin ya duba dakuna kamar yadda ya saba inda ya tsinci gawar Muniat.
Bayan ganin hakan ne yasa mai kula da masaukin bakin yayi gaggawar sanar da caji ofis din Ikorodu, bayan nan ne jami’an ‘yan sanda su ka ci gaba da bincike.