Shekarar 2020 shekara ce wadda tazo da wasu kalar abubuwa musamman yadda cutar Coronavirus ta girgiza duniya inda harda harkokin wasanni ta haɗa inda daga ciki harda ƙwallon ƙafa.
Sai dai duk da haka wasu ‘yan wasan sunyi ƙoƙari sun nuna bajinta ta wajen jefa ƙwallaye da kuma taimakawa a jefa ƙwallo a zare wato sun nuna bajinta kamar yadda aka saba a kowacce shekara.
Ga jerin ‘yan wasan kamar haka:
1. Lewandowski da cin ƙwallaye da taimakawa a jefa ƙaallaye yayi sau 49.
2. Leonel Messi yayi sau 36.
3. Eirlin Braut Halaand yayi sau 35.
4. Christiano Ronaldo yayi sau 35.
5. Romelo Lukaku yayi sau 33.
6. Muller yayi sau 32.
7. Kai Havartz yayi sau 32.
8. Mbappe yayi sau 31.
9. Bruno Fernandez yayi sau 31.
Amma kuma daga cikin 31 da Bruno Fernandez yayi akwai bugun daga kai sai mai tsaron gida guda 12 wato Penalty.