Mai horar da ƙungiyar Al-Nassr ta ƙasar Saudiyya, Rudi Garcai, ya bayyana a inda Cristiano Ronaldo zai kammala taka leda.
Rudi Garcia ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo zai koma nahiyar Turai kafin ya daina buga kwallo, inda yayi nuni da cewa ɗan wasan ba zai kawo ƙarshen buga kwallor sa a ƙasar Saudiyya ba. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Mijina yana matuƙar so na amma na kamu da soyayyar wani daban, ku taya ni addu’a -Wata matar aure
A cikin watan da ya gabata ne dai ɗan wasan ya koma ƙungiyarta Al-Nassr a kan wata kwantiragin maƙudan kudaɗe.
Mai horar da shi a yanzu Rudi Garcia yayi nuni da cewa ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’or har sau biyar, zai koma nahiyar Turai kafin ya daina buga kwallo.
Garcia ya bayyana hakan ne bayan da Al-Nassr ta sha kashi da ci 3-1 a hannun ƙungiyar Al Ittihad, a wasan kusa da na ƙarshe a gasar Arabian Super Cup, wasan da Ronaldo ya kasa taɓa zare.
Tsohon ɗan wasan na Manchester United da Real Madrid har yanzu bai zura kwallo ko ɗaya ba a gasar Saudi Pro League.
“Samun Cristiano Ronaldo abu ne mai armashi saboda yana taimakawa wajen rikita ƴan baya.”
“Ronaldo yana daga cikin ƴan wasan da suka fi iya kwallo a duniya. Ba zai kammala buga kwallon sa a Al-Nassr ba, zai koma nahiyar Turai.” A cewar Garcia.
Ancelotti Na Shirin Daukar Dzeko da Icardi zuwa Real Madrid
A wani labarin na daban kuma mai horar da Real Madrid na son kawo wasu zaratan ƴan wasa guda biyu a kulob ɗin.
Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya bayyana tsohon dan wasan Manchester City Edin Dzeko da tsohon dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Mauro Icardi a matsayin ‘yan wasan da zai dauka don karfafa gwiwar kungiyarsa.
A cewar El Nacional, Ancelotti yana so ya kawo Dzeko da Icardi zuwa Real Madrid don ƙarfafa kai hari, saboda Karim Benzema yana fama da rauni.