
Mai horas da yan wasan kasar Denmark ya ragargaji Uefa ne bisa nuna rashin ko’inkula kan batun Dan wasan.
Dan wasan kasar Denmark Erikson ya yanke jiki ya fada a tsakiyar wasa, inda nan take masu kula da lafiya suka haukansa don bincikan halinsa.
KARANTA:-
Wasu mahara sun hallaka mutane 26 a Jihar Zamfara
Dole tasa anyi waje da Dan wasan don tafiya dashi asibiti ganin yanayisa ya ta’azzara.
Mai horas da yan wasan yace akwai damar daga wasa awa 48 kamin a fara wasa idan akwai yiwuwar kamuwar yan Wasa da cutar numfashi, Amman idan cutar kwakwalwace hakan bazaiyuwu ba
Ya bukaci shuwagabanin kula da harkokin wasannin dasu bayarda wata mafita Wanda zai Kare faruwar hakan nan gaba.
A WANI LABARIN:-
Jami’an yan sanda a Jihar Katsina sun cafke wani yaro dan shekara 13 busa zargin hallaka wasu yan fashi daji biyu a Jiharu yan fashi daji biyu a Jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa yaron mai suna Abdulkareem Mati a baya ya kasance yana yiwa gawurtaccen dan fashin dajin nan Ardo Nashaware aiki, a wani gandun daji Birnin Magaji dake Jihar Zamfara.
Kakakin rundunar yan sandar Jihar Gambo Musa ya shaida cewa jami’an nasu sun cafke yaron ne bayan ya tsere daga gandun dajin da ya ailata kisan.
Sai dai Mati ya bayyana cewa an dauke shi ne da zummar zai taimaka wajen kiwon shanu, amma aka karkatar da hankalinsa zuwa sarrafa bindiga kirar AK47 tare da maida shi mai kula da mutane da aka yi garkuwa da su.
Gambo Isah ya ce kazalika yaron ya shaida musu cewa cin zarafi da musgunawa da manyan yan fashin dajin ke yi masa ne ya harzuka shi har ya dauki AK47 ya bindige biyu daga cikinsu.
Yanzu haka dai ana cigaba da Gudanar da bincike kam yaron don ganin me ya dace da shi a dokance