Tsohon dan wasan tsakiya n Kungiyar Kwallon Kafa ta BArcelona Xavi Hernandez ya bayyana Kcoin Tawagar Kasar Jamus Joechim Low a matsayin Kcoin daya tilo da zai iya rike Barcelona har ya kai ta gaci idan ya ajiye mukamin sa na horas da kasar ta Jamus.
A yan baya-bayan nan ne Low ya bayyana abniyar shi ta sauka daga mukamin horas da kasar ta Jamus biyo bayan jinkiri da aka samu wurin fafata wasan karshe na kofin kasashen nahiyar turai.
Kocin mai shekara sittin da daya ya fara aikin horas da Jamus ne tun a shekarar 2006 in da ya kai ga tawagar lashe gasar Kofin duniya ta 2014 yayin da ya lashe kofin zakarun kasashe a shekara ta 2017.
Hakan ya sa tsohon dan wasan na Barcelona wanda kuma ake alaknbta shi da hadewa da tsohuwar kungiyar tashi ya ce Low shine kadai zai iya haurawa da kungiuyar izuwa tudujn na tsira.
Kwantiragin Joechim Low zai kare da Jamus ne a shekara ta 2022 too sai dai ya ce ba zai iya ci gaba da jagorantar tawagar ba biyo bayan rashin katabus a shekarar da ta gabata.
A shekarar da ta gabatar dai dakyar Jamus ta samu ta lallaba ta yi nasara a wasanni uku cikin takwas da ta fafata, wanda a ciki ne kasar Spaniya ta markade ta 6:0 cikin gasar kasashe ta Nations League da ya zamo rashin nasara mafi muni ga kasar tun shekarar 1931 da kasar Austria ta yi mata dukan kawo wuka makamanciyar wannan..