Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ingantaccen shugabanci bai shafi jam’iyyun siyasa ba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Wike ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da titin Ogbunuabali-Eastern Bypass wanda wani jigon jam’iyyar APC Sanata Aliyu Wamakko ya yi a ranar Talata.
Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su yi tunanin cewa shugabanci aiki ne na jam’iyyun siyasa, alhalin abin ya shafi tunanin mutum ne.
Yar Wasa Serena Williams Ta Sanar da Ritayarta daga buga Kwallon Tennis
“Shugabanci ba na jam’iyya bane, shugabanci na mutum ne, Jam’iyya tsani ce kawai don aiwatar da burin ku, don samun damar gaya wa mutanenku ina da wannan ƙarfin, Ina da wannan ingancin da zan yi muku.
Idan ka dauke ni yau daga PDP zuwa wata jam’iyya, har yanzu zan yin abunda nayi niyya, don haka, ba don ina cikin PDP ba ne.
Wike ya bayyana cewa kauna, sha’awar sa da jajircewarsa na yi wa mutanen Rivers hidima sun bambanta shi da sauran ‘yan siyasa.
Shi ya sa, in ji shi, akwai ci gaba da himma wajen kara kima ga rayuwa, yin tasiri ga sauyi tare da juyin juya hali na samar da ababen more rayuwa da inganta jihar.
Wike ya ce yayin da wasu suke yin amfani da matsalar tattalin arziki a matsayin uzuri don ba da shugabanci da yi wa jama’arsu hidima, ya sami wata hanya mai kyau don ci gaba da kai ayyukan a Rivers.
Kalaman na Wike na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin ya dabaibaye jam’iyyar PDP da kuma yunkurin sasanta shi da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.