Ko’odinetan Gaggamin yankin Neman zaben Buhari, Alhaji Danladi Pasali, ya rasu.
Pasali ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja a ranar Talata da yamma.
Ali Pasali, kanin mamacin, ya tabbatar da rasuwarsa a Jos, babban birnin jihar Filato.
Shekaru biyu da suka gabata Pasali ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya yi kira da a gaggauta hukunta wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar juyin juya hali na RevolutionNow, inda ya ce ‘yan Najeriya sun fi wayo a yanzu kuma ba za su taba bari wata kungiya ko jama’a ta yaudare su da wani abin da bai dace da hadin kai ba, da kuma zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Pasali ya ce kira na tayar da zaune tsaye da sauya gwamnati ta hanyar amfani da duk wata hanya ba zabe ba ba komai ba ne illa cin amanar kasa don haka ya kamata jami’an tsaro su dauki matakin.
Ya ce kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya bayyana karara yadda za a sauya mulki a tsarin dimokuradiyya, wato ta hanyar babban zabe.
“Najeriya ta gudanar da da’irar zabe, wanda Sowore da sauran ‘yan siyasan adawa suka gwada farin jininsu a rumfunan zabe, Amma Basu dace ba. A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da aikin na karshe na zaben wanda shi ne sauraron korafe-korafe da suka shafi zabe a kotun koli a fadin kasar nan.”
“Me ya kawo wannan gaggawar? Dangane da abin da ya shafi mu, wannan shi ne aikin wasu ‘yan siyasa masu takaici da wawashe dukiyar mu da suka yi hasarar kudaden shiga a sakamakon yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin yanzu ke yi,” in ji Pasali.