Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa Manchester United da 3 da 1 wasan gab da na karshe a gasar Kofin FA.
Chelsea ta samu wannan nasarar ne bayan kuskuren da mai tsaron ragar Man United David de Gea ya yi har sau biyu da kuma cin gida da Harry Maguire ya yi.
Chelsea a yanzu dai za ta buga wasan karshe a gasar da kungiyar Arsenal a ranar 1 ga watan Agustan 2020.
A duk karawa uku da aka yi tsakanin Manchester United da Chelsea a kakar wasa ta bana, Chelsea ta yi nasara a duka sai wannan kawai ta samu nasara.
Olivier Giroud da Mason Mount sune wanda suka bai wa Chelsea wannan nasarar.