Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya ce za su iyakar kokarinsu wajen dawo da tarihin kungiyar domin ganin sun yi nasara kan manyan kungiyoyi daidai lokacin da ya ke shirin tunkarar Manchester City a wasan gab da na karshe na cin kofin FA.
A yau Asabar Arsenal ta ke shirin karawa da Manchester City a filin wasa na Wembley da ke Landan, inda Arteta ke cewa tawagarsa a shirye ta ke tsaf don tunkarar wasan.
A haduwar Arsenal da Manchester City 7 a baya-bayan nan Arsenal ba ta iya nasara a wasa ko daya ba, inda City ta lashe dukkaninsu tare da ratatawa Arsenal din kwallaye 20 a haduwar 7 inda Arsenal ta iya zura kwallo 2 cal.
Rabon Arsenal da nasara kan City tun haduwarsu cikin 2017 kuma yanzu haka Cityn ce ke rike da kofin wanda ke nuna abu ne mai wuya ta yi sakaci ya bar gidanta musamman bayan da ta rasa na firimiya a hannun Liverpool.