By Ishaq Dabai
Ana zargin Wani matashi mai kimanin shekaru 21 mai suna Muhammed Yusuf, da kashe maihaifinsa a sakamakon dukan kawo wuka da yayi masa biyo bayan shan miyagun kwayoyi da yayi a Jihar Kogi.
Wanda ake zargin yace ya dade da mahaifin nasa a lokacin da ake zargin ya hadu dashi a makarantar furamare ta St. Mary dake Lokoja a ranar laraba da daddare.
A cewar wani makwabcin sa mai suna Miss Bello Nana yaro ya ce sun sami sabanin fahimta tun a ranar laraba da safe, inda ya bukaci mahaifin nasa daya kai rahoto zuwa ofishin ‘yan Sanda su kama shi tun kafin matsalar ta faru.
Yace wanda ake zargin ya kammala makarantar sakandire ta SSSC inda yace mahaifin nasa yana tsananta masa, duk da kwarin gwiwar da mahaifin nasa yake bashi amma ya cigaba da shan kwayar.
Nana tace ”a ranar da abun zai faru na tafi aiki da misalin karfe 4 na yamma inda nake tashi karfe 12 na dare, amma ranar sai ban kai karfe sha biyun ba na tashi da karfe 10 na yamma ne, sai kawai na taho gida na kwankwasa kofar gida babu wanda ya bude.”
Tuni dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sanda na jihar DSP Williams Aya ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama wanda suke zargin. Kazalika ya kara da cewa tuni dai suka garzaya dashi asibitin dake Lokoja inda kuma suka damke mai laifin.