By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Kogi tace ta kama mutane hudu da laifin aikata garkuwa da mutane da kuma aikata fashi da makami inda suka addabi mazauna karamar hukumar Bassa.
Sanarwar tana kunshe cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Williams Ayah ya fitar yace sun kama wanda suke zargin da alburusai da bindiga kirar gida guda daya da harsashi mai ci Zangon milimita 7.62 da kuma kirar G3 guda daya sannan kuma da kokon kai na mutum biyu.
“Kama masu garkuwa da ‘yan fashin ya biyo bayan samun bayanai daga jami’an ‘yan Sanda na musamman da sukayi inda suka zagaye kewayen da suke a maboyar su dake Jerusalem Oguma dake Bassa kuma suka sami nasarar kamesu karkshin jagorancin DPO na yankin.
“Masu laifin da aka kama sun hadar da Guda Dangana, Dogo Chure, Dekina Zhiya, Samson Nyizo, wanda dukkanin su ‘yan karamar hukumar Bassa ne.” a cewar sanarwar.
Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar CP Idrisu Dauda Dabban ya baiwa jami’an nasa Umarnin da su maida hankali wajen aikin nasu inda ya bukaci mutanen jihar ta Kogi da sudinga baiwa jami’an tsaro masaniya dan kawar da masu aikata manyan laifuka a jihar.” a cewar sa.