Gwamnatin Jahar Kogi a ranar Juma’a ta nemi Hukumar Hana Zagon Ƙasa-EFCC, data nemi afuwar ta akan ƙarar data shigar da jahar akan zargin cinye Naira biliyan 20 kuɗin bashin da jahar ta ciwo.
A ranar 31 ga watan Ogustan Shekarar 2021, Babban Jojin Jahar Lagos Tijjani Ringim, ya bada umarnin garƙame asusun jahar Kogi na Bankin Sterling, biyo bayan wata ƙara da EFCC ta shigar kafin ta janye.
Hukumar hana zagon ƙasar tayi zargin cewa kuɗin da za’ayi amfani dashi wajen albashi ma’aikatan jahar, amma an ajiye su a wani asusu da suna ‘Kogi State Salary Bailout Account’.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Matan harkar fim, su na komawa fitsararru inji Furodusa Bashir Abubakar Maishadda
A zama Kotun da akayi a ranar Juma’a, Kemi Pinheiro lauyan EFCC, ya buƙaci a tsaida cigaba da shari’ar.
“Shuwagabancin Bankin Sterling inda wani asusu mai lamba 0073572696 da suna asusun kogi na Albashi ya daɗe a bankin, kuma babu wani indai na gaskiyane sai wannan asusun.
Dayake jawabi a ranar Juma’a a lokacin bada lambar yabo ta ƴan jarida da suka cinye wata gasar rubutu, Kingsley Fanwo kwamishinan Ilmi na Kogi yace abun baƙin ciki ne cewa EFCC ta yarda da ayi hayar ta domin cimma wani muradi.
Fanwo ya bayyana kuɗirin EFCC a matsayin abun kunya, inda yace Hukumar taƙi sauraron bayanai da dama da Gwamnatin Jahar tayi mata akan al’amarin, amma ta yarda cewa, gwamnatin ta ajiye biliyan 19 a wani banki.
Kwamishinan ya ɓuƙaci EFCC data riƙa amfani da kwarewa da ƙa’idoji a lokacin da take gudanar da aikace-aikacen ta.
Fanwo ya ƙara dacewa, jahar zata yiwa manema labarai jawabi bayan ta karɓi kwafin hukuncin da kotu tayi.