Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu kananan yara guda uku a karamar hukumar Ajaokuta da ke jihar Kogi. Suna neman kudin fansa Naira miliyan100.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Ayah, ya tabbatar da sace mutanen a ranar Juma’ar nan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Edward Ebuka ya tura jami’an ‘yan sanda daban-daban da ke yaki da masu garkuwa da mutane tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta domin zakulo masu garkuwa da mutane ne domin kubutar da yaran tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
An yi garkuwa da yaran uku masu shekaru tsakanin uku, biyar, da shekaru goma a yammacin Larabar da ta gabata da misalin karfe takwas na dare a gidansu na Kaduna Estate Ajaokuta Steel Township, da wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ba.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/rashin-tsaro-sarkin-bichi-ya-shirya-taron-adduoin-samun-zaman-lafiya-a-jihar-kano/
Rahotannin da shaidun gani da ido suka bayar sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen da ke dauke da bindigogi sun yi ta harbe-harbe don tsoratar da mazauna yankin kafin su yi awon gaba da yaran.
Wani dan uwa da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar a safiyar ranar Alhamis sun tuntubi ‘yan uwa inda suka bukaci Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.
Lamarin dai na zuwa ne kwanaki bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biyar a Jida-Bassa da ke karamar hukumar Ajaokuta a jihar Kogi.
Sai dai a wani mataki na dakile kalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar Kogi, gwamnan jihar Yahaya Bello ya bayar da umarnin rufe dukkan gidajen karuwai tare da haramta amfani da abin rufe fuska a wuraren taruwar jama’a domin tantance mutane.
(CHANNELS TV)