Wasu ‘yan banga sun bi sawu tare da kubutar da wasu mutane biyu masu suna Sa’idu Aliyu da Usman Ibrahim da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Akyar da ke karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi.
Wani mazaunin unguwar, mai suna Shuaibu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 9:34 na safe lokacin da wadanda abin ya shafa suka je gona da babur uku don yin lodin gawayi.
Wadanda abin ya shafa dai sun shagaltu da lodin gawayi ne sai ga ‘yan bindigar dauke da makamai suka fito suka tafi da su.
Ya ce wani manomi da ke aiki a gonarsa ya hango ‘yan bindigar, inda ya koma ya sanar da ‘yan bangan garin, inda suka bi ‘yan bindigar.
A cewarsa, masu garkuwa da mutanen da suka ga ‘yan bangan suka fara harbe-harbe a kan Mai Uwa da wabi, inda aka yi ta harbe-harbe a tsakanin bangarorin biyu.
Ya ce daga baya masu garkuwa da mutanen sun gudu suka bar wadanda suka sace.
Wani dan banga da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun yi watsi da wadanda suka kama ne bayan da suka yi galaba a kansu a yayin fafatawar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Ovye Aya, har yanzu bai samu amsa kiran waya ko amsa sakonnin tes da aka aika masa don tabbatar da faruwar lamarin ba, har zuwa lokacin da aka buga labarin.