Wasu mutanen kauye biyu da aka yi garkuwa da su a unguwar Orobomi da ke karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi sun samu ‘yanci bayan sun biya kudin fansa naira miliyan 1.4 ga wadanda suka sace su.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba, 2021 suka mamaye kauyen Orobomi inda suka kashe wani matashi tare da yin garkuwa da wasu mutane biyu masu suna Ibrahim da kuma Salihu.
Wani dan uwan wadanda abin ya shafa mai suna Saidu Salihu ya ce an sako su ne a ranar Talata da yamma da misalin karfe 8:12 na dare kusa da dajin Osuku da ke makwabtaka da Kpareke tare da yankin Kotonkarfe a jihar Kogi.
Ya ce tun da farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 10 bayan sun yi tattauna da juna, inda ya ce iyalan wadanda aka sace, sun tara Naira miliyan 1.4 bayan tattaunawa mai tsanani.
“Iyalin sun sayar da wasu kadarori, ciki har da wasu amfanin gona, don tara Naira miliyan 1.4 don biyan kudin fansa,” in ji shi.
Ya ce mutanen biyu da aka kashe a halin yanzu ana kan duba lafiyarsu a wani asibiti da ba a bayyana ba a Lokoja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Ovey Ayah, bai dauki waya ko amsa sakon da aka aike masa ba game da lamarin.