Gwamnatin Kogi a ranar Laraba ta bayyana kudurinta na ciwo bashin dala miliyan 100 domin ganin ta gudanar da wadansu ayyuka da za su bunkasa ci gaban tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan kudi da tsare-tsare na jihar, Idris Ashiru shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Lokoja jin kadan da kammala zaman majalisar zartaswar jihar, inda ya ce jami’ai daga jihar za su je majalisar Dattijai domin kare wannan kudurin.
Ya ce idan har suka yi nasarar karbo wannan bashin, daga cikin ayyukan da za su yi harda farfado da kamfanin sarrafa hatsi na SCPZ dake Alape a karamar hukumar Kabba/Buni dake jihar.