By Ishaq Dabai
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA na kasa Brig Gen Buba Marwa ya bayyana jindadinsa dan gane da kin amincewa da majalissar dokoki tayi na halatta dokar noman tabar Wiwi.
Marwa yayi wannan jawabin ne ga manema labarai bayan kammala tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Villa a Abuja.
A cewar sa kaso 90℅ na ‘yan majalissun kasar nan basu bada goyan bayan halatta dokar noma tabar wiwi ba, saboda sun san babu inda kundin tsarin mulki ya nuna hakan.
“A yanzu haka kungiyar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cewa tabar wiwi tana taba lafiyar kwakwalwa, da amfanin da kwakwalwa take, sannan tana shafar halayyar dan adam kuma tana taba lafiyar sassan jiki baya da haka tana haifar da ciwo daga karshe takai ga kashe mutum.
“Baya da haka tabar wiwi tana cutar da lafiya sannan hatsarice a cikin al’umma, saboda doka bata bada damar amfani da ita ba, a kalla Najeriya tana da mutane miliyan 10.6 wadanda suke ta ammali da tabar wiwi, wanda hakan yasa Najeriya take a sahun farko na masu shan tabar wiwi a duniya, wannan ba’abin bakin ciki bane?”in jihi.