Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce wasu muhimman kayyayaki na zaben 2023 suna hannun babban bankin Kasa CBN.
Kwamishinan na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na INEC, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan ga wakilinmu a ranar Talata.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Idan dai ba a manta ba a shekarar 2022 mutane da kungiyoyi sun nuna matukar damuwa game da tsarkin kayan zabe da ke hannun CBN, bayan da labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ke nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a kasar.
KARANTA HAKANAN Za Mu Shiga Tattaunawa Kan Ajiyar Kayan Zabe Da CBN — Kwamishinan INEC
Sakamakon haka, Shugaban hukumar zabe ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu, a ranar 4 ga watan Yunin 2022, ya ce a halin yanzu ba za a sake amfani da kayan zabe ta hanyar CBN ba.
Shugaban na INEC ya bayyana cewa hukumar zabe ba ta taba samun wata matsala da CBN ba tun da aka fara hulda, amma saboda “halin da ake ciki yanzu” za a samu wani zabin.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Sai dai Okoye ya bayyana cewa hukumar ta buga tare da isar da galibin kayan da suka dace, kamar sakamako da katunan zabe, sannan ta ajiye su tare da CBN don tafiya zuwa ofisoshin kananan hukumomin hukumar a fadin kasar.
Ya kuma bayyana cewa INEC ta kusan kammala jigilar kayayyakin da ba su da muhimmanci a fadin kasar nan.
Da yake bayanin yadda za a kai muhimman kayyayaki gabanin zabe mai zuwa, Okoye ya ce, “Hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris na 2023. Hukumar ta karbi cikakken tsarin tantance masu kada kuri’a na na’urar BVAS a runfunan zabe 176,846 a Najeriya.
“Za a tura BVAS zuwa dukkan rumfunan
zabe in ban da rumfunan zabe 240 wadanda ba su da masu kada kuri’a. Hukumar ta karbi ragamar aikin yi wa kananan hukumomi 8,809 rajista da kananan hukumomin kasar nan 774.
A Wani Labarin Kuma Kora: Jigon PDP Ya Kai Karar Jam’iyyar, Da Ayu, Ya Sake Marawa Tinubu Baya
Tsohon gwamnan jihar Enugu kuma sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta gabas, Chimaroke Nnamani, ya maka jam’iyyar PDP a kotu kan matakin ladabtarwa da aka yi masa bisa zargin cin zarafin jam’iyya.
Wakilinmu ya tattaro cewa Nnamani ya shigar da karar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar 7 ga watan Fabrairun 2023, kwanaki kadan kafin ficewar sa daga jam’iyyar.