Komai da ya Shafe ka Karya ce – Bode George ya caccaki Tinubu
Wani jigon jam’iyyar PDP, Bode George, ya bayyana jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, a matsayin ” tarin maƙaryata.
George ya ce duk abin da Tinubu ya dangana wa kansa ” karya ne”.
Ya ce Tinubu bai yi wani abu ba don rage radadin mazauna jihar Legas duk da cewa ya yi gwamna na wa’adi biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Yiwa Allah Ku Daina Tallata Yan Rashawa– Shugaban EFCC Ga Kafafen Yada Labarai
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a daren jiya, George ya ce: “Ba ni da wata damuwa, kuma ba ni da wata rigima da Tinubu, amma abin da na sani shi ne duk abin da ya ce shi ko sunansa ne wannan ko kuma makarantarsa shi ne tarin karya.
“Ni dan Legas ne mai gaskiya, mun san yadda Legas take, kuma Legas ita ce cibiyar kasuwanci, ba kawai a Najeriya ba, har ma a yammacin Afirka baki daya. Me wannan mutumin ya yi mana?”
Jigon na PDP ya bukaci Tinubu ya bude baki kan mallakar kamfanin Alpa Beta.
Ya ce kamata ya yi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya shaidawa ‘yan Najeriya nawa kamfanin ya sata a gwamnatin jihar Legas.
“Na yi tambaya mai sauƙi kuma babu ɗayansu da ya iya amsa ta: wanene ya mallaki kamfanin Alpha Beta? Nawa ne kamfanin Alpha Beta ya sace daga asusun ajiyar mu a jihar Legas?
“Me ya yi don rage radadin da al’ummar jihar ke ciki?” Ya tambaya.