Salihu Tanko-Yakasai, tsohon mai taimakawa gwamna Abdullahi Ganduje na Kano kan harkokin yada labarai, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Tanko-Yakasai ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter a ranar Talata.
Ya ce sanarwar tasa a hukumance za ta gudana ne a ranar Juma’a, inda ya kara da cewa zai tsaya takara a jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP).
“Da sunan Allah, Kuma da sunan sa dogara; babu karfi & babu dabara sai ga Allah. Yan uwa da abokan arziki da masoyana wannan shine in sanar daku aniyara ta, ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kano karkashin babbar jam’iyyar mu ta PRP. Sanarwar ta a hukumance za ta kasance ne a wannan Juma’a, ”kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Hakan na zuwa ne makonni kadan bayan da ya yi murabus daga mukaminsa a jam’iyyar APC.
A watan Fabrairun shekarar 2021, Ganduje ya kori Tanko-Yakasai saboda “ci gaba da maganganun da ba basu dace ba” da kuma sukar Shugaba Muhammadu Buhari.
Tanko-Yakasai, yayin da ya bar jam’iyyar APC a watan Maris, ya ce jam’iyyar Mai Mulki ta kasa, ta gaza wajan cika alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya a yakin neman zabe.
A wani labarin Kuma na daban.
Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne an banka musu wuta inda suka kone kurmus a garin Kanshio da ke wajen garin Makurdi a jihar Benue.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, an bi su ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda aka kama su daura da makarantar Divine Mercy Minor Seminary da ke Kanshio inda a karshe aka kona su.
An tattaro cewa wadanda ake zargin wadanda tun farko su uku ne amma daya daga cikinsu ya tsere a lokacin da ake binsa, sun samu shiga wani gida da karfi da yaji a garin Kanshio a kokarinsu na yi wa dangi fashi bayan sun yi harbin gaggawa don kaucewa shiga tsakani.
Sai dai kuma sa’a ya ci karo da su, inda aka ce shugaban gidan ya yi ta maza inda ya kama daya daga cikinsu, lamarin da ya sa sauran mutanen biyu suka shiga tsakani da wannan jarumin har suka kubutar da abokin aikin nasu.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wadanda ake zargin bayan ceto dan kungiyar nasu ne suka gudu ta hanyar tsallaka katanga inda suka hau kan babur da ke jiran su a bakin titi amma wadanda abin ya shafa suka nemin taimakon mazauna yankin lamarin da ya jawo hankalin wasu matasa da ke yankin.
Matasan dai kamar yadda aka samu sun fatattaki wadanda ake zargin har ta kai da biyu daga cikinsu suka makale a kusa da makarantar Seminary inda nan take suka banka musu wuta yayin da sauran suka tsallake rijiya da baya ta katangar makarantar suka tsere.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Benue PPRO, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.
“An tabbatar da al’amura. Ana ci gaba da bincike, don Allah, ”in ji Anene a cikin wani sakon rubutu.
Comments 1