Rundunar sojojin Koriya ta Arewa ta sanar da harba makami mai linzami cikin tekun da ya hade yankin Koriya gabanin komawa teburin tattaunawa tsakaninta da Amurka da za a gudanar a karshen wannan mako.
Jim kadan bayan harba makamin ministan tsaron Kasar Japan Taro Kono ya bayyana cewar makamin da Koriya ta Arewan ta harba ya sauka a yankin hada-hadar tattalin arzikin Japan. bayan firaiminista Shinzo Abe ya bayyana wannan mataki da Koriya ta Arewa da dauka a matsayin karya dokokin Majalisar Dinkin Duniya, tare da shan alwashin ci gaba da goyon bayan Amirka da sauran kasashe don kare al’umma da kuma zama cikin shiri.