A ranar Litinin ne gwamnatin Koriya ta ce za ta samar da dala miliyan 12.4 don gina kananan cibiyoyin Wutar Lantarki masu amfani da hasken rana a cikin al’ummomin Najeriya.
Mataimakin shugaban cibiyar bunkasa fasahar kere-kere ta kasar Koriya ta Kudu Kim Jeong-Wook ne ya bayyana hakan a Abuja.
Jeong-Wook ya ce an tsara aikin ne domin biyan bukatuwar makamashin da al’ummomin karkara ke yi ta hanyar gina na’urorin samar da wutar lantarki masu amfani da hasken rana tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya.
Ya ce aikin zai bunkasa tattalin arzikin cikin gida, samar da ayyukan yi, yaki da talauci da inganta rayuwar Yan Nigeria.
“Bugu da ƙari, ta hanyar Samar da ingantattun makamashi tsakanin birane da yankunan karkara, ana sa ran aikin zai haifar da daidaiton ci gaba a fadin kasar,” in ji shi.