Jaridar AljazirahNigeria ta labarto cewa kayayyakin abincin da aka ce a rabawa marasa galihu domin tallafa su sakamakon cutar Koronabairos a Nijeriya, ana zargin wadansu hukumomi sun maida abin kasuwanci a jihar Akwa Ibom.
Majiyar tamu ta ce an gano hakan ne bayan da Talakawan jihar suka fara korafi, inda suke zargin hukumomin da karkatar da tallafin suna siyarwa a maimaikon bai wa Talakawan.
AljazirahNigeria ta ce Gwamna Udom Emmanuel kwanaki bakwai da suka gabata ya kaddamar da shirin tallafawa Talakawan da kayan masarufi. A lokacin kaddamarwar, Sakataren gwamnatin jihar, Dr. Emmanuel Ekeuwem, ya ce kayayyakin abincin sun hada da shinkafa, gari, Fulawa, wanda za a raba a tsakanin kauyaku 3, 000 a fadin kananan hukumomi 31 dake jihar.
Sai dai a wani bincike da majiyarmu din ta ce ta yi ta gano cewa Manajan da ke lura da ma’ajiyar abincin a Akwa Ibom, ya maishe da abin kasuwanci. Inda a wata murya da aka nada aka ji yana tattauna cikin harshen Ibo yadda zai siyarwa da wata mata ‘yar kasuwa buhunhunan shinkafa.