Musulmi a jihar Legas, babban birnin kasuwancin kasarnan za su gudanar da sallolin Juma’a karon farko cikin watan hudu tun bayan barkewar annobar cutar korona.
Bayanai sun nuna cewa kuma, a karon farko bayan wata hudu a ranar Lahadi, suma Kiristoci za su gudanar da ibadu a coci-coci.
Tun a cikin watan Maris aka rufe masallatai da coci-coci sakamakon annobar korona.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce za a sake bude wuraren ibada ne sakamakon ci gaban da ake samu a yakin da jihar ke yi da cutar korona.
Sai dai za a bar wuraren ibadar ne kawai su kyale kashi 50 na mutanen da suka kamata su gudanar da ibada domin shiga su gudanar da ibada.
Gwamnati ta ce dole ne masu ibada su dauki matakan kariya kamarsu sanya takunkumi da nesa-nesa da juna.